Wednesday, September 1, 2010

TATTAKI CIKIN WASU WAKOKIN DOKTA SHATA KATSINA

Yau kusan shekaru 10 kenan da duniya ta rasa mutumin daya kirkiro ya kuma kawo sauyi a hidimar kidan kalangu a kasar hausa.Bama ana zato ba, a’a a fagen wakar hausa ba wani a gabansa har ya zuwa tatassara. Shata, Duna na Bilkin Sambo.Koda yake akwai mawaka da sukayi zarra a zamaninsa amma hada basirarsa da tasu tamkar hada hasken kyandir ne da hasken rana.A tsakanin 1936 da 1999,watau farawa da gama wakarsa(ko kuma tsakanin wakarsa ta farko:’yammaza Allahn fara bamu……..’ da wakarsa ta karshe:’Dankabo Jarmai Mamman……..’,wadda yayi lokacin nadin Alh.Ummaru Musa Gwamnan Katsina ranar 29/5/1999) Shata yayi wakoki kimanin abinda ya dara 8,000.Dalili shine ni kaina na taba rutsa shi a gida Funtuwa na tambayeshi ko nawa ne wakokin Alhaji?Sai yace baya iya ganewa amma yasan tun sa’adda ya fara yayi wakoki kundi-kundi har kundi sama da 40,kuma a cikin kowanne kundi yana da waka sama da 200. In ka tara kaga zaya baka jimillar da aka bayyana sama. Zanso in dan tazgada kadan in nazarci abinda mawaka suka kira ‘sare’ a waka, wanda da shi mawaka sukayi ta aron wakokinsa suna gina nasu kalmomin..’Sare’ a waka na nufin ka ari waka ko wani sashe na wakar wani mutum ka maishe shi naka. Amma saboda wasu mawakan ma suna da basira wadda take da amfani kwarai sai kaga wasu lokuta kalmomoin Shatan da nasu sunyi kamanni da juna. Akwai da dama a inda wakokin makadin da na wasu sukazo iri daya. Misali, a cikin 1940 Bawa makaho mai ganga na Gorar Fata ya saukar wa Indon Zara,wata budurwa da tayi tashe,diyar maigarin ‘Yammama.Anan ya sami labarin wani bakon mawaki waishi Shata ya bulla Ketare.Bayan wasan ‘Yammama ya kare suka fusata suka doshi Ketare don su kai ma Shata caffa su yakeshi.Suna sauka Ketare sai bama bata lokaci gaba daya suka zama yaran Shatan.Kwana biyu a Ketare ana wasa.Da zasu koma gida sai Shatan ya yi tsalle ya bisu.Ya tafi dasu saboda a dan zaman da sukayi da shi a Ketare ya shaku da Bawa sosai. Wata rana a Gora sai ga wani direba daga Jikamshi yazo daukar Bawa don yin bukinsa, na auren wata yarinya,Hauwa ‘yar Tsohuwa.Aka dauke su aka tafi dasu. Wakar da Bawan yayi: ‘Ado Dan Ma’inna goshin Jirgi kanen Barau’,itace tazo iri daya da wata da waka da Shatan ya taba yiwa Akawu Na Guga mai Biri da Barewa’,inda shi kuma yake cewa:’Jefa kidan Na Guga koba girma da arziki’.Daga baya kuma ya dauki amshinta yayi wa Bawa Janke direba na Musawa,inda yake cewa: ‘Jirgin sama Bawa Tashi koli ka tsere na Laraba’Yayiwa direbobi da dama wakoki da salon wannan amshin. Daga baya ya dauki irin amshin kuma yayi wa su Bello Maitama da wani direba Dan Kaura wakoki. Shata bazai taba mancewa da Muhammadu Dankura sarkin Bege makadin sarkin Daura Abdulrahman ba,saboda bashi ma da babban aboki cikin makada kamarsa. Shima Dankura mai basira ne kwarai. Ya taba yiwa Sarkin Daura Abdulrahman ubangidansa wata waka mai shigen ‘Sadauki Shehu Magajin Mamman’ irin ta Shata.Kada a manta cewa Shata yayiwa manyan iyayen gidansa irin su Sardauna Gamji(1957),Haru Dan Kassim Kano(1956),marigayi hakimin Musawa Usman Liman(1952) da dai wasu da dama wakoki da irin wannan amshin. Ya’u wazirin Shata shine babban yaron makadin, da suka hadu a Bakori cikin 1943. Amma a sannan Ya’u makadi ne mai zaman kansa. Sai a cikin 1959/1960 suka hade da Shatan, lokacin shi kuma ya taso daga Kano. Shima Ya’u fasihi ne matuka, don yama yi wasu wakoki wadanda sukayi kamanni da wasu wakokin Shatan. Kafin kuma su hade ya sha daukar wasu kalmomin Shatan yana gina nasa, kamar daga wakokin: Soja iyalin Gwamna’(1967), ‘Dan Leko Baban Leko’(1966), ‘Tijjani Hashim Dan-iya’(1986), ‘Don sallah da salatil fatihi ………’(1962), ‘Haji Iro Babangida’(1985), ‘Ya Alhaji Babba Dan kamasho’(25/12/1980). Har karshen rayuwarsa Shata ya samu biyayya daga mawaka danginsa da dama.Saboda kashi 95 na mawakan Najeriya da ma wajenta suna aron kalmomin Shata dama wakokinsa suna gina nasu kalmomin wakokinsu. Sani mai kuntigi Gusau wani mutum ne da yayi yayi a Da. Shima ya ari wasu kalmomi daga Shata ba ma dai irin wakokin Bakandamiya(alo-alo mai ganga ya gode……(1959/1960),da ‘Dan Zabarma ya kyauta, Dan Zabarma yallabai’(1961),da ‘Yallabai yallabai yallabai ‘yar kankanuwa kankane’(1955) duk wakokin Sani mai kuntigi Gusau ne asalin su. Ya’u Wazirin Shata yace saboda shima mai hazaka ne wasu wakokin sa sunyi kamanni da na Shatan. A zamanin yaki(1967-1970) Ya’u yayi wakoki na siyasar kasa.Ba wani gidan rediyon da yafi fifita Shata fiye da gidan rediyon Tarayya na Kaduna.Musamman da makadin ya tafi Nijar a cikin 1959 akayi fira dashi akace wai yayi wa Sardauna wani tsokaci da baiyi wa mutanen NPC dadi ba.To wannan Magana ita tasa Shata yayi ban iska da wadanda ke dasawa dashi cikin ‘yan gidan sarautar Kano dama wasu jama’ar NPC. Alhali kage ne sukayi masa da kuma haushinsa da suke ji. Suka fusata suka juya masa baya.To Wamban Daura Bashar shi yayi ta kokari har ya daidaita Sardaunan da shi Shata. Tun cikin shekarun 1950 jami’o’in kasashen Turai da Amurka suka fara nazarin wakokin makadin.A wasu jami’o’I a Jamus ana nazarin wakokin Mamman Shata. A Jami’ar Kalifoniya ma wasu turawa kusan su 6 sunyi nazarin mawakin,in ka debe manazartanmu na gida, irin su Abdulkadir Dangambo da Farfesa Danbatta,wanda a cikin 1975 ya rubuta kundin digiri na 3 a jami’ar Indiyana,Amerika akan wakokin makadin. A shekarar 1972 shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ya aika aka kirawo shi daga kasar Nijar, suka hadu a Kano ya gaisheshi ya bashi lambar yabo.Ranar 15/10/1976 ma gwamnatin tarayya ta bashi lambar yabo mai suna MON,shi da Garba ABCD(shi kuma aka bashi lambar OFR). Cibiyar tunawa da James Coleman na Jami’ar Kalifoniya ma ta bashi lambar yabo sa’ilin da ya ziyarci can a cikin 1989.Akwai ma kananan lambobi da kungiyoyi suka bashi a garuruwa kamar Funtuwa da Kano da dai sauransu. Kashe maigirma Sardauna a cikin 1966 yasa wakokin Shata sun dauki wani sabon salo,na yi wa sojoji da ‘yan boko wakoki don basu kwarin gwuiwa don a tafi bakin daga. Don sai da aka kashe su Sardauna das u Abubakar Tafawa Balewa muka fahimci a Arewa an barmu a baya.Wakokin Shata suka zaburar da ‘yan Arewa. An tsakuro wannan ne daga littafin Aliyu Ibrahim Kankara,mai suna ‘Mahadi Mai Dogon Zamani: Shata Da Kundin Wakokinsa’.

1 comment:

  1. I am so overwhelmed by you. Just of recent I listened to your old interviewed by freedom Radio as far back as 2011 and I am lucky to search for you and your writing about Shata. I really love Shata music ever since I was a child I.e since 1970 up to. As ad now I had in my collections his music more than 1000. I want to have more pls help me.My name is Mustapha Muhammad Tahir of Kano State Pension Fund Trustees PMB 3482 Kano. Mustymuhdtahir016@Gmail.com

    ReplyDelete