Sunday, September 5, 2010

Bayajidda Da Rashin Tabbacin Zuwansa Kasar Hausa

Bayajidda na da wani muhimmin gurbi da hausa da Bahaushe suka ware masa a cikin tarihinsa da al’adarsa. Saidai tarihinsa da zuwansa qasar hausa din yana da jefa mutane cikin wasu-wasi na shin wai da gaske ne ma kuwa anyi shi? Ance sunansa Abu Yazid, amma da farko ma dai banda shi kanshi Bayajidda din ance anyi wani Abu Yazid xin da shima akace yayo hijira daga can inda akace wannan Bayajiddan ya fito shima. Na farko: tarihi ya nuna cewa wai ya fito daga Bagdad ta Gabas ta tsakiya, yazo Barno wai har ya auri wata xiyar sarkin can, amma da suka yo arewa sai nakuda ta haihuwa ta kamata. Wai sai akace ya ajiyeta nan ya sa wasu su tsareta don ta haihu, shi sai yayo arewa ya yi linzami a Daura, wai cikin hijira ta 619 AD. Amma ba inda aka nuna daga bisani ga zuru’o’insu shi da wannan mata. Zancenshi da wannan mata nan ya tsaya bai kuma ci gaba ba, wanda ya kamata ace tarihi ya nuna ga jikokinsa da wannan mata. Na Biyu: ance da yazo Daura ya auri Gimbiya Daurama, a sanadiyyar kashe macijiya mai suna ‘sarki’ ran wata alhamis, to da ya rasu har yanzu ba inda akace ga kabarinsa. Mutanen da suka shahara a Duniya an san kaburburansu amma mutum biyu ne a fage ba a ga kaburburansu ba; na malam Bayajidda da na madam Amina sarauniyar Zazzau. Na Ukku: Zancen hausa 7 da banza 7 wannan kaima kasan ba abin ma yarda ba ne, don bama ta yiwuwa ace ‘ya’yan da Bayajiddan ya haifa da Daurama wai su sune hausa 7, wadanda kuma ya haifa da kishiyar da yayi mata daga baya wai sune banza 7. To wai ma sai akace hausa 7 su suka fara sarautar garuruwan qasar hausa. Ma’ana, Daura ita ta haifi sauran garuruwan qasar hausa. Anya kuwa wannan zancen gaskiya ne? Kuma banza 7 su suka fara sarautar garuruwan kasar kudu. Banza 7 sune: Yoruba, Ibibiyo, Kwararrafa, Gwari da sauransu.Babu tabbacin wannan zancen don ba inda Daura ta samo alaqa da waxannan qasashe na kudu. Na Hudu:Ita kanta gimbiya Daurama akwai alamar tambaya akan wasu zantuttuka a game da ita. Ba wai nace aba ayi taba, amma da akace su 6 duk mata ne kuma xakinsu xaya su suka sarauci qasar Daura.Ya za ace mata 6 a jere suna sarauta ba tare da surkawa da wani namiji ba? Ita Daurama itace sarauniya ta qarshe, a cewar tarihin. Sannan akace waisu Dauramar Larabawa ne. Yaya Balarabe ya samu yankowa ya wuto duk garuruwan nan ya kutso cikin wannan lungu mai zurfi mai suna Daura? Na Biyar: A tarihin, wai xan da Bayajidda ya haifa da Daurama na farko mai suna Bawo shi ya haifi Kumayau, wanda ya fara sarautar Katsina. Kenan ana nufin Daura ta girme ma Katsina.Nan ma akwai alamar tambaya, saboda Katsina na da daxaxxen tarihi, tun kafin ma zuwan musulunci, zamanin da ake bautar iskokai da rana da itatuwan tsamiya. Shi Bayajidda ance ya zo Daura cikin shekara ta 619 AD kaga zamanin Annabi Muhammadu (SAW) kuma a lokacin ba a fara binciken tarihin baqar fata ba bare a tabbatar da e lallai yaje Daurar.

8 comments:

  1. hakika wannan blog naka ya kayatar da ni,kuma ina rokon ALLAH ya kara basira

    ReplyDelete
  2. Tabbas wannan bayane sun kayatar dani,kuma naji dadin karantawa.

    ReplyDelete
  3. to me za ka iya bayar wa a matsayin tarihin hausawa maimakon na bayajidda da ka rushe?

    ReplyDelete
  4. This comment has been removed by the author.

    ReplyDelete
  5. Wannan gaskiya ne, ya kamata a sake yin nazari da bincike dangane da wannan kagaggen labarin, na zuwan Bayajida.

    ReplyDelete
  6. JOIN ILLUMINATI TODAY ALL YOUR WISH WE GRANTED,Do you want to be a member of Illuminati as a brotherhood that will make you rich and famous in the world and have power to control,people in the high place in the worldwide.Are you a business Man or Woman,Artist, Political,Musician,Student,do you want to be rich,famous,powerful in life,join the Illuminati brotherhood cult today and get instant rich sum of.2 million dollars in as benfite,and a free home. any where you choose to live in this world and also get 2,000,000 U.S dollars monthly as a salary.Call to Mr.Roy and just join us and get all benefits.morganilluminatirich@gmail.com or whatsspa +2347051758952

    ReplyDelete
  7. Tarihi da asalinta da shi ake alfahari dama ai tarihin bahaushen ƙagagge ne .
    Arashin uwane ake uwar ɗaki, amma ai agola bayacin gado.
    Ba rishe tarihin akayi ba gaskiyace aka faɗa dan haka kai ka nemo tarihin gaskiya da zai gamsar damu mukuma zamu yarda indai gaskiyar ce.

    ReplyDelete